Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul Baiti (AS) – ABNA - ya habarta cewa: majiyoyin yada labarai sun bayar da rahoton wasu sabbin hare-haren makamai masu linzami da dakarun kasar Iran suka kai kan yankunan da aka mamaye.
Bisa labarin da aka samu, an kai wasu hare-haren makamai masu linzami a birnin Tel Aviv, babban birnin gwamnatin Sahayoniya. Daga cikin wuraren da aka kai hari a wannan zagaye na hare-haren har da ma'aikatar tsaron Isra'ila a Tel Aviv.
An kuma tabbatar da harin da aka kai hedkwatar ma'aikatar tsaron Isra'ila ta hannun 'yan jaridun na kasa da kasa a yankunan da ta mamaye.
Sahayoniyawa suna amfani da mafi girman takaita yada hotuna da bidiyo da ke fitowa daga Tel Aviv. Dangane da haka ne sojojin Isra'ila suka bukaci mazauna matsugunan yahudawan sahyoniya da kada su dauki hoton bidiyo da hotuna na makami mai linzami da Iran ta kai kan yankunan da ta mamaye.
.........................
Your Comment